Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Lagos ya kaddamar da jirgin ruwa na Yaƙi (Seaward Defence Boat (SDB III) wanda rundunae sojojin ruwan Najeriya suka samar dashi.
Wannan shine jirgi na uku wanda ake kera a Nigeria ta karkashin Kamfanin Naval Dockyard Limited dake Lagos.
Da yake jawabi a yayin kaddamar da jirgin Shugaba Buhari yace, samar da Sabbin Jiragen ga Mayakan Ruwa zai kara musu Ƙwarin gwiwar yin aiki tukuru domin ganin an samar da tsaro a tashoshin jirgin ruwa na Nigeria.
Shugaban ya hori dukkan Jami’an Sojojin ruwan da su ci gaba da nuna kwarewar su da tabbatar da yin aiki da Sabbin Jiragen da aka ƙera ta hanyar data dace.












































