Yanzu-Yanzu: ADC ta zabi Amaechi a matsayin abokin takarar Atiku

Atiku Abubakar right and Rotimi Amaechi 670x430

Jam’iyyar hadaka ta ADC ta zabi tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takarar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2027.

Jam’iyyar ta ce amincewa da Amaechin ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi da kuma yadda ya zo na biyu a zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar ta ADC da kuma tarihin hidimar sa a gwamnati.

Da yake sanar da hukuncin a cikin wata sanarwa ranar Litinin, Sakataren Yada Labaran ADC na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya bayyana tikitin Atiku-Amaechi a matsayin “tikitin hadin kai da ceto” wanda zai iya magance kalubalenda Najeriya ke fuskanta.

“Hadin gwiwar da ake shirin yi tsakanin Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi ya wuce hadin siyasa kawai, haduwar manyan ‘yan siyasa biyun da aka taba gwadawa, masu gogewa, suna da tasiri a fadin kasa da kuma iya jagoranci da ake bukata don ceto Najeriya daga kalubalen da take ciki yanzu da sake daidaita kasar zuwa sabon tsari na wadata, tsaro, da ci gaba ga kowa,” in ji Abdullahi.

A cewar jam’iyyar, gogewar Amaechi ta siyasa da gudanarwarsa ta sa ya cancanta wannan matsayi, ganin ya taba zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ribas, Gwamnan Jihar Ribas wa’adi biyu da Ministan Sufuri.

“Kadan daga cikin ’yan siyasa a Najeriya ne suke da irin wannan gogewa da daidaito a bangarorin majalisa da na zartarwa na gwamnati. Wannan gogewa zata zama mai matukar amfani wajen goyon bayan sabuwar gwamnatin ADC daga ranar farko,” in ji sanarwar.

ADC ta kuma ce tasirin Amaechi a Kudu maso Kudu da fadin Kudancin Najeriya zai karfafa tikitin da kara yadda ake karba a fadin kasa.
Jam’iyyar ta bayyana kwarin gwiwa cewa wannan hadin gwiwa zai ba da hadin kai ga kawancen ta da karfafa goyon baya gabanin zaben 2027.

“Shugabancin ADC yana da kwarin gwiwa cewa wannan hadin gwiwa zai ba wa kawancenku duk abin da ya kamata, zai ja hankalin ‘yan Najeriya da kuma ba da jagorancin da ake bukata don gina Jamhuriyar Tarayyar Najeriya mai karfi, mafi tsaro da wadata,” in ji sanarwar.

ADC ta yi kira ga mambobin jam’iyyar, abokan kawance, kungiyoyin jama’a, kungiyoyin matasa da mata, da sauran ‘yan Najeriya su goyi bayan kamfen din su yayin da ake fara shirye-shirye don zaben gama gari na 2027.:

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here