Dan majalisar mai wakiltar mazabar Tarauni Hafizu Ibrahim Kawu ya bayyana farin cikinsa bisa Karbar sama da Naira miliyan 20 domin siyan fom din takara daga masu ruwa da tsaki da kuma wasu kungiyoyi.
Ƙungiyoyin da suka Tallafa sun kunshi kungiyoyin Yan kasuwa da na Dalibai, da wadanda suka ci gajiyar ayyukan Dan majalisar da shugabannin jam’iyyar APC sai manyan jami’an gwamnati da shugabannin Kananan hukumomin biyu da sauransu.
Dan majalisar ya yi alkawarin ba zai yi kasa a gwiwa ba, wajen ci gaba da gudanar da ayyuka masu nagarta domin karfafa gwiwa ga wadanda suka yi masa wannan tagomashi da kuma samarwa Jama’a sauki.
Da yake jawabi a madadin masu ruwa da tsaki,Babban mataimaki ga Gwamnan Jihar Kano, kan harkokin siyasa, Alhaji Mustapha Mai Hula, ya ce tallafin ya zama dole domin Hafizu Kawu ya ci gaba da samar da ci gaba da ba a taba ganin irinsa ba a mazabar.
“Mun san cewa yana da kudin siyan takarar tsayawa takarar, amma ba za mu bar shi ya saya wa kansa ba.
Mun tara kudin ne ta hanyar bayar da gudunmawar Naira 10,000, a lokuta mabambanta”.
Mai Hula ya kuma bayyana cewa Hafiz Kawu ya canza salo da rayuwar jama’a da dama ba wai a mazabar sa ta tarayya kadai ba, harda Jihar Kano baki daya.
Dan majalisar wanda zai sake tsayawa takara a karo na biyu, ya bada tabbacin cewa zai kara yin kokari fiye da wannan lokacin matukar ya koma majalisar ta hanyar samar da ababen more rayuwa da inganta rayuwar jama’a tare da ci gaba da inganta abubuwan da aka cimma kawo wannan lokacin.
“Manufata ita ce ci gaba da samar da ayyukan ababen more rayuwa da bunkasa jarin al’umma tare da ci gaba da inganta ayyukan da muka yi a cikin shekarun da suka gabata wadanda suka ba wa ‘yan mazabarmu karfin gwiwa, har ta kai ga tara wannan kudi don tallafa mana kawai don ci gaba da kuma tabbatar da cewa mun ci gaba yin wakilci mafi kyau.”













































