Bikin Salla: Hukumar NSCDC za ta baza jami’ai 3,023 don tabbatar da an gudanar da bukukuwan Sallah lafiya a Kano

Hukumar, NSCDC, zargi, bisa, badakalar
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC ta kama wani matashi mai matsakaicin shekaru a jihar Ondo bisa zargin badakalar biza.Kwamandan NSCDC a jihar...

Yayin da ake gab da fara gudanar da bukukuwan Salla, hukumar tsaro da Civil Defence NSCDC shiyyar Kano, ta ce, ta tura jami’ai dubu uku da ashirin da uku domin tabbatar da gudanar da bukukuwan Salla cikin lumana.

Kwamandan hukumar na jihar, Malam Idris Adamu Zakari, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar DSC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce, an zaɓo ma’aikatan ne daga sassa daban-daban da kuma kwamandojin yanƙi da suka haɗa da jami’an sirri.

Adamu Zakari ya buƙaci jami’an da su tabbatar da cikakken tsaro tare da tunkarar duk wata barazana ta tsaro a kowanne lungu da saƙo na jihar lokacin bukukuwan sallar har ma da bayanta.

“Za a ba da kulawa ta musamman ga wurare masu mahimmanci da suka ƙunshi filayen Idi, kantina wuraren shaƙatawa da wuraren da ke da muhimman kadarori,” in ji shi.

Kwamandan na yi wa daukacin al’ummar musulmi barka da Sallah tare da kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani yunƙurin bata-gari ga jami’an tsaro mafi kusa domin ɗaukar matakin gaggawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here