Shugaba Buhari na jagorantar taron Majalisar Koli ta Kasa domin tattauna batutuwan da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.
A na sa ran taron Majalisar da ke gudana a Fadar Shugaban Kasa zai tattauna kan matsalar mai, sauyin kudi, karancin takardun Naira da kuma sha’anin tsaro gabanin babban zabe da za a yi nan da mako biyu.
Taron ya samu halarcin tsoffin shugabannin kasa irin su, Abdulsalami Abubakar, Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo, da kuma Yakubu Gowon da gwamnoni da kuma Shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa.
Majalisar Koli ta Kasa wani bangare ne Gwamnatin Najeriya da ke ba da shawarwari kan tsare-tsaren gwamnati a bangaren zartaswa.










































