Pakistan da Iran sun daidaita tsakanin su ta fuskar diflomasiyya

Solacebase Logo
Solacebase Logo

Ofishin muƙaddashin Firaiministan Pakistan Anwar ul – Haq Kakar ya ce alaƙar diflomasiyya ta dawo tsakanin Pakistan da Iran bayan kai wa juna hare-hare.

Ana sa ran jakadun ƙasar za su koma bakin aikinsu nan gaba kaɗan.

Karanta wannan: Gwamnatin Kogi ta haramta bada lasisi ga masu hako Ma’adanai a Jihar

Sai dai har yanzu Iran ba ta ce komai ba kan wannan batu.

Duka ƙasashen biyun sun yi wa jakaduunsu kiranye bayan hare-haren makami mai linzami da jirage marasa matuƙa kan masu ikirarin jihadi da ke zaune a kan iyakokin ƙasar biyu.

Iran ta kai hari kan yankin Balochistan a ranar Talata, inda Pakistan ta ce harin ya kashe mutum biyu.

Bayan nan Pakistan ta kai nata harin a ranar Alhamis, Iran ta ce lamarin ya yi ajalin mutum tara.,

A safiyar ranar Juma’a, a wata tattaunawa da ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu suka yi ta wayar tarho, Pakistan ta nuna tana son aiki tare da Iran a kowanne irin lamari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here