Kungiyar Pantamiyya ta bayyana goyon baya ga Gwamna, ta yi kira da hadin kan APC a Gombe

Pantami

Kungiyar Pantamiyya ta bayyana goyon bayanta ga burin takarar gwamna na dan takarar jam’iyyar APC a Jihar Gombe, Dakta Jamil Isyaku Gwamna, gabanin babban zaben 2027.

Wannan ci gaba na kunshe cikin wata sanarwa da Mataimakin Gwamna kan harkokin yada labarai, brahim Sani Shawai, ya fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce amincewar kungiyar ta dogara ne kan karbuwar da Gwamna ke samu a cikin APC da tsakanin magoya baya a matakin kananan hukumomi dama Jihar Gombe baki daya.

Yayin ziyar nuna goyon baya da ya kai wa Gwamna, Sanusin Gombe ya bayyana ganawar a matsayin mai muhimmanci da dacewa da lokaci, inda ya ce kungiyar ta himmatu wajen tallafawa “fitowar wanda ya cancanta” wanda zai iya karfafa nasarorin da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya samu.

A cewarsa, kwarewar siyasar Dakta Gwamna, alakarsa da mutanen kasa, da karbuwarsa a sassa daban-daban na jam’iyyar sun sanya shi ya zama dan takarar da ya dace da aikin da ke gaba.

“Mun zo ne domin nuna goyon baya da himma ga aikin tabbatar da cewa APC ta ci gaba da kasancewa cikin hadin kai da samun nasara a 2027.

Gwamna ya nuna tawali’u, kwarewa, da iya tafiya da kowa tare da shi,” in ji shi.

Kungiyar ta kuma yi kira ga tsohon Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami, da sauran ‘Yan takara a zaben fidda gwanin gwamna na APC da su goyi bayan Dakta Gwamna domin maslahar hadin kan jam’iyya da ci gaban Jihar Gombe.

Sanusin-Gombe ya jaddada cewa hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da nasarar APC a zaben gwamna da na shugaban kasa.

Da yake martani, Dakta Gwamna ya mika godiyasa ga Kungiyar Pantamiyya bisa abin da ya kira sanya hadin kan jam’iyya gaba da muradun kansu, yana cewa ziyarar ta nuna nasarar siyasa da himma ga makomar APC a jihar.

Ya tabbatar wa mambobin jam’iyyar cewa zai bi salon shugabanci da zai yi tafiya da kowa, ciki wanda zai iya daukar dukkan muradu da ra’ayoyi daban-daban a cikin jam’iyyar.

Dakta Gwamna ya kuma kira ga tsoffin ‘yan takara da masu ruwa da tsaki da su sanya bambance-bambancen da suka tsakanin daga zaben fidda gwani a gave, su yi aiki tare don ci gaba da tafiyar da ci gaban da gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta samu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here