Shugaban Hukumar kula da aikin hajji ta Kasa (NAHCON), Ambasada Ismail Yusuf, ya ce rage kujerun aikin Hajjin 2026 da aka yi wa Najeriya mataki ne da ya shafi kasashe da dama, ba wai iya Najeriya kadai ba.
Yusuf ya bayyana haka ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, inda ya danganta matakin da iyakar daukar alhazai da kuma sabbin tsare-tsaren da hukumomin Saudiyya suka bullo da su.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Abdulbasit Abba, ya fitar, Yusuf ya bukaci jihohi da su gyara rahotannin da ke cewa an ware Najeriya wajen rage kujerun.
Ya jaddada kudirin NAHCON na gudanar da aiki cikin gaskiya da kwarewa tare da bin ka’idoji yayin da shirye-shiryen Hajjin 2026 ke kara kankama.
Ya ce adadin kujerun da aka ware wa Najeriya ya kai alhazai 40,250, ba tare da hada da kamfanonin yawon bude ido ba, amma bayanan da aka tura sun wuce adadin da aka amince da shi.
Saboda haka, ya umarci jihohi da su daidaita bayanansu cikin gaggawa tare da cire sunayen da suka wuce kima domin kauce wa tsaiko a harkokin gudanarwa.
A cewarsa, hukumomin Saudiyya sun sanya ranar 1 ga Shawwal a matsayin wa’adin karshe na fitar da biza, kuma babu alamun za a kara lokaci.
Memba mai wakiltar Ma’aikatar Lafiya a Hukumar, Dakta Said Dumbulwa, ya yi bayani kan sabbin ka’idojin takardar shaidar lafiya.
Dumbulwa ya ce dole a gudanar da gwajin lafiya a asibitocin da aka amince da su kadai, tare da saka lambar rajistar Medical gwajin a takardun, sannan a loda su ta hanyar tsarin zamani domin tantancewa.
Ya kara da cewa ba a ba asibitoci masu zaman kansu damar bayar da takardar shaidar Hajji ba, tare da bayyana shirin samar da wata kafa ta kasa domin daidaita harkokin lafiya.
A wani sassauci ga alhazai, Yusuf ya sanar da rage kudin Yellow Card daga Naira 5,000 zuwa Naira 2,000 domin Hajjin 2026.
Ya kuma ce Hukumar Lafiyar Tashoshin Jiragen Sama da Ruwa za ta kula kai tsaye da batun shaidar allurar rigakafi, bisa tsauraran matakan da Saudiyya ke dauka ciki har da na’urar tantance bayanan halittu.
Hukumar ta kuma bayyana cewa za ta sa ido sosai kan yadda kamfanonin jiragen sama ke gudanar da ayyukansu, tare da gargadin cewa wadanda ba su yi yadda ya kamata ba za a iya kwace musu rabon kujeru a ba wasu.
An shawarci jihohi da su gaggauta mayar da kudin wadanda ba za su samu damar tafiya ba domin kauce wa rikice-rikice da kuma kare amincewar jama’a.
Yusuf ya ce za a tura tawagogin sa ido zuwa Saudiyya domin duba batutuwan abinci, masauki, tsafta da sauran ayyukan hidima.
Ya jaddada cewa Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi ce ke da alhakin kula da alhazai, yayin da NAHCON ke da rawar sa ido da tsara dokoki.
Ya yi kira da a hada kai da nuna kwarewa domin tabbatar da nasarar Hajjin 2026.













































