Hukumar Kula da Basussuka ta Kasa (DMO) ta bayyana cewa jimillar bashin da jihohin Najeriya 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT) suke bi ya kai tiriliyan N4.002 zuwa ranar 30 ga Satumban 2025.
Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa bashin na jihohi da FCT ya kai kashi 2.61 cikin dari na jimillar bashin gwamnati na kasa da ya tsaya a Tiriliyan 153.29 a daidai wannan lokaci.
Bayanan sun nuna cewa bashin ya fi yawa a wasu jihohi kalilan, inda jihohi 10 suka dauki kashi 67 cikin dari na daukacin bashin, wanda ya kai Tiriliyan 2.68.
Jihar Legas ce ke kan gaba a yawan bashi da tiriliyan N1.045, wanda ya kai kusan kashi 26 cikin dari na bashin da dukkan jihohi da FCT ke bi.
Jihar Ribas ce ta biyu da bashin biliyan N381.205, sai Jihar Delta da Biliyan 247.171.
Jihar Enugu ce ta hudu da Biliyan N194.715, yayin da jihohin Ogun da Bauchi ke da bashin Biliyan 168.093 da Biliyan 158.197 bi da bi.
Jihar Neja na da bashin Biliyan 143.469, sai Jihar Kuros Riba da Biliyan 141.941 da kuma Jihar Benuwe da Biliyan N107.254. Jihar Akwa Ibom ce ta goma a cikin jihohin da suka fi yawan bashi da Biliyan N95.506 zuwa Satumban 2025.
Alkaluman na nuna karuwar matsin lamba kan kudaden jihohi.
A gefe guda kuma, Gwamnatin Tarayya ce ke dauke da mafi yawan nauyin bashin gwamnati gaba daya.
Wannan bashi na jihohi ya samo asali ne daga gibin kasafin kudi da kuma bukatar samar da ababen more rayuwa, tare da raguwar kudaden shiga daga man fetur.
Wasu nazarce-nazarce sun nuna cewa karbar bashi a matakin jihohi na taimakawa wajen cike gibin kasafi, amma idan ba a kula ba zai iya kawo tangarda ga bunkasar tattalin arziki.
Yawaitar bashin a jihohin da ke da arzikin man fetur ko manyan birane kamar Legas na kara fito da batun tsarin rabon kudaden kasa, inda ake kira da a kara bai wa jihohi damar samar da karin kudaden shiga tare da tsaurara sharuddan karbar bashi.
Haka kuma, karuwar bashin na nufin karin kudin ruwa da ake biya, lamarin da ke rage kudaden da za a kashe a fannoni kamar lafiya da ilimi, musamman a yanayin faduwar darajar naira da hauhawar kudin ruwa.
Ana sa ran gyare-gyare kamar kara habaka kudaden shiga na cikin gida da kuma tallafin gwamnatin tarayya za su taimaka wajen rage matsin lambar, sai dai alkaluman jihohin da suka fi yawan bashi na nuna bukatar kara tsaurara kula da harkokin kudi.













































