Yanzu-yanzu: Kamfanin mai na Dangote ya dakatar da sayar da fetur da naira

Dangote Refinery

Kamfanin man fetur na Dangote ya sanar da dakatar da sayar da fetur da kuɗin naira, matakin da ya jefa masu rarraba mai cikin rudani tare da haifar da sabbin damuwa kan tsadar mai da matsin tattalin arzikin musayar kuɗaɗe.

A wata wasiƙa da aka tura wa abokan cinikin kamfanin da misalin ƙarfe 6:42 na yamma a ranar Juma’a, an bayyana cewa matakin zai fara aiki daga Lahadi, 28 ga Satumba, 2025.

Sanarwar, wacce sashen gudanar da harkokin kasuwanci na Dangote ya sanya wa hannu, ta yi take da cewa: “Dakatar da Sayar da DPRP PMS da Naira – Fara aiki daga 28 ga Satumba, 2025”.

Kamfanin ya kuma roƙi abokan cinikin da ke da cinikayyar da aka kulla da naira su nemi maido musu da kuɗinsu.

Duk wani abokin ciniki da ke son maidowa da kuɗin da ya biya a naira ya gabatar da buƙatar maido da kuɗinsa.”

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin ya shiga rikici da ƙungiyoyin kwadago bayan korar fiye da ma’aikata ‘yan Najeriya 800, lamarin da ya tayar da ƙura da kira ga gwamnati ta shiga tsakani.

Labari mai alaƙa: Matatar Man Dangote ta tabbatar da korar ma’aikata

Ƙungiyar ma’aikata ta PENGASSAN ta zargi kamfanin da yin abubuwan cin zarafi ga ma’aikata, tare da yin barazanar gudanar da yajin-aikin ƙasa baki ɗaya idan ba a warware matsalar ba.

Ba wannan ne karo na farko ba da kamfanin ya dakatar da sayar da man fetur da naira. A watan Maris 2025, Dangote ya taɓa ɗaukar irin wannan mataki, yana mai cewa rabon mai da kudin naira da ake ba shi bai wadatar da buƙatar cikin gida ba.

A wancan lokaci, lamarin ya haddasa tashin farashin mai a matakan tasha zuwa kusan N1,000 a kowace lita.

Dakatarwar ta kuma zo a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar tashin hankali a masana’antar, lamarin da ya jefa ɗimbin masu amfani da mai cikin damuwa tare da ƙara shakku kan yiwuwar tsadar rayuwa a Najeriya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here