Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bayyana cewa ta fara bincike kan wani faifan bidiyo na zargin fyade ga daliban makarantar Chrisland da ke Legas.
Mai magana da yawun Rundunar, SP Benjamin Hundey, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda yace Kwamishinan Yan sandan Jihar ta Legas CP Abiodun Alabi, ya bada Umarnin gudanar da bincike kan Lamarin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya hakaito cewa a cikin Faifen Bidiyon na wata Yarinya Mai shekaru 10 Yar Makarantar Chrisland, an yi zargin cewa Daliban Makarantar sun yi mata Fyade lokacin da suka je Ziyarar ilimi Birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa daga Makaranta.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a Birnin na Dubai, lokacin da Daliban suka ka yi Balaguro zuwa can domin halartar Gasar wasannin makarantu ta Duniya a ranakun 10 zuwa 13 ga watan Maris na shekarar 2023, har ma suka samu nasarar lashe kyautuka fiye da 30.
Hundey ya ruwaito Kwamishinan ‘yan sandan na cewa binciken zai gano sunayen ‘yan wasan da ke cikin faifan bidiyon, da hakikanin abin da ya faru a faifan bidiyon, da kuma wurin da lamarin ya faru.
Kazalika, binciken zai kawo karshen zargin barazanar rayuwa da ake yi wa dalibar makarantar da kuma gwajin da ake zargin an yi mata na daukar ciki fiye da sau daya ba tare da izinin iyayenta ba.
Ya kuma bada tabbacin cewa za a ci gaba da bin diddigin lamarin don tabbatar da cewa ba a tafka kura-kurai ba.













































