Gwamnoni 5 na jam’iyyar PDP da suka yiwa dan takarar shugaban kasan jam’iyyarsu, Atiku Abubakar, tawaye zasu sanar da wanda zasu goyawa baya a zaben 2023.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wadannan gwamnoni karkashin gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers zasu sanar ne ranar Alhamis, 5 ga watan Junairu, 2023.
Gwamnonin sun hada da gwamnon Nyesom Wike (Rivers), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia), Samuel Ortom (Benue), da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.













































