Fafaroma Benedict yana cikin matsananciyar jinya – Fafaroma Francis

322801193 715799786575388 5320219060473297340 n
322801193 715799786575388 5320219060473297340 n

Fafaroma Francis ya ce tsohon fafaroman da ya gada wato fafaroma Benedict na cikin matsananciyar rashin lafiya, inda ya buƙaci masu ziyarar ibada a cocin Vatican da su sanya shi cikin addu’o’insu.

A shekarar 2013 ne dai tsohon fafaroman mai shekara 95, ya zama babban shugaban ɗarikar Katolika na farko da ya sauka daga muƙaminsa cikin shekarar 600, inda ya ce ya sauka daga muƙamin nasa ne saboda shekaru.

A ƙarshen huɗubar da ya gabatar wa mabiya a cocinsa ne dai fafaroma Fransis ya buƙace su da sanya tsohon fafaroman cikin addu’o’insu na ibada.

Daga baya ne kuma fadar vatican ta ce rashin lafiyar tsohon fafaroman ta tsananta.

A farkon wannan watan ne fafaroma fransis ya ce yana yawan ziyartar tsohon fafaroman domin duba lafiyarsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here