
Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da sama da Naira miliyan 23 domin horar da daliban da suka yi rijistar jarrabawar SSCE na shekarar 2024 a jihar.
Dokta Abbas Abubakar, Babban Sakataren Hukumar Ilimi ta Jihar Jigawa ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga masu gudanarwa da ko’odinetoci da kungiyoyi.
Abubakar ya ce jimillar dalibai 37,037 da za su kammala karatunsu na karshe a jihar za su ci gajiyar wannan atisayen a fannin Lissafi da Ingilishi.
Karin labari: Shugaba Buhari ya bawa ministan ilimi mako biyu ya kawo karshen yajin aikin ASUU
Ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Alhaji Badaru Abubakar ne ya kaddamar da shirin a shekarar 2019 domin baiwa daliban damar cin jarabawar kammala SSCE da maki mai kyau.
Sakataren zartaswar ya kara da cewa za a fara horas da karin watanni biyu kafin a fara SSCE da hukumar shirya jarrabawa ta WAEC da kuma ta NECO.
A cewarsa, ana sa ran masu gudanarwa 365 na harshen Ingilishi da 365 na ilmin lissafi, ko’odinetoci 204 da kuma kungiyoyin sa ido 197 ne za su shiga cikin shirin domin a samu nasarar aiwatar da shi.
Karin labari: Ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargi da garkuwa da mutane a Abuja
Abbas ya bayyana fatan cewa wannan karimcin zai baiwa wadanda suka ci gajiyar damar samun kimar da ake bukata domin shiga jami’o’i da sauran manyan makarantun kasar nan.
Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a karin kocin da su tabbatar da amincewar da aka yi musu ta hanyar yin abin da ake bukata daga gare su.
A nasa jawabin kwamishinan ilimi mai zurfi Dakta Yusuf Chamo ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na ci gaba da bullo da tsare-tsare da zasu bunkasa ilimi.
Karin labari: Rundunar sojin Najeriya ta bayyana dalilin fasa gidan Yarin Kuje
Chamo ya kara da cewa karin horon zai tafi tare da taimakawa daliban su samu nasara da maki mai kyau a cikin darussa guda biyu kasancewar manyan abubuwan da ake bukata don samun damar shiga manyan makarantu.
Don haka ya bukaci masu gudanarwa da kodinetoci da kungiyoyin sa ido kan wannan atisayen da su yi aiki tukuru domin ganin an samu kyakykyawan aiki, musamman a muhimman batutuwan guda biyu.