Jami’ar Nasarawa tayi watsi da yajin aikin ASUU, inda zata koma bakin aiki

9bb1726bd4b93744
9bb1726bd4b93744

Da alamun za’a koma karatu a jami’ar Nasarawa State University Keffi (NSUK) bayan gwamnatin jihar ta yi alkawarin fara biyansu albashinsu daga baitul mali.

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana hakan yayin zaman majalisar zartaswa jihar ranar Labara a gidan gwamnatin jihar.

Injiniya Sule yace sun yanke shawarar daukar nauyin biyan albashin Malaman ASUU saboda haka zasu koma aji, rahoton ChannelsTV. A cewar gwamnan, gwamnatin zata fara biyan albashin Malaman fari daga watan nan.

Ya kara da cewa shugabannin jami’ar, kungiyar ma’aikatan SSANU da NASU duk sunyi alkawarin komawa bakin aiki.

“Daya daga cikin sharrudan da suka bamu shine mu dau nauyin biyan albashin dukkan ma’aikatan jami’ar, saboda su daina amfani da kudin shigarsu.” “Da muka duba baitul malinmu, mun ga akwai isasshen kudi kuma saboda muhimmancin da muka ba ilimi, zamu fara biya daga wannan watan.”

“Kuma muna kyautata zaton cewa idan muka biyasu ranar Alhamis ko Juma’a, zasu koma aji.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here