Kungiyar malaman jami’o’ i ta kasa ASUU, ta nemi da ayi wata doka wacce zata hana ‘yan siyasa kai ‘ya-‘yan su kasashen waje domin yin karatu.
Shugaban kungiyar reshan jami’ar jihar Delta, Farfesa Kingdom Tombra, ya bayyana hakan yayin gudanar da zan-ga-zangar da kungiyar NLC ke yi domin marawa ASUU baya, ranar Talata a Yenagoa.
“Yin dokar zai bawa jami’o’ in Najeriya dama su cigaba yacce ba’a tunani, sanin kowa ne yajin aikin da mukiye, bawai muna yi bani don muzgunawa ‘ya ‘yan talakawa, muna yine domin cigaban karatun su.”
“Idon har ‘ya ‘yan talakawa zasu je makaranta daya da ‘ya ‘yan masu kudi, bana tunanin za’a kara yajin aiki a kasar nan.” Inji shi.