Zaben 2023: Babban dan Kwankwasiyya ya kuma jam’iyyar APC a Kano

BC382302 ECF6 4C0E ABFA F4D79D0688AA 614x570 1 614x430 1
BC382302 ECF6 4C0E ABFA F4D79D0688AA 614x570 1 614x430 1

Mabiyin Rabi’u Musa Kwankwaso, Dakta Umar Tanko Yakasai, ya ajiye tafiyar Kwankwasiyya inda ya koma Gandujiya.

Yakasai wanda yana daya daga cikin manya manyan ‘yan Kwankwasiyya ya fita daga jam’iyya ta NNPP, inda ya kuma APC a ranar Talata.

Solacebase ta rawaitu cewa Yakasai ya bar NNPP zuwa APC ne saboda kasan ciwar Nasiru Yusuf Gawuna, dan takarar gwamna a jam’iyyar ta APC.

Ya kara da cewa Gawuna shi kadai ne wanda yake da kwarewa kuma ya dace ya zama gwamanan Kano

“Yanke shawarar danayi ta marawa Gawuna baya, ba wai abune wanda ya faru haka kawai ba, abune wanda na lura da abubuwa da dama kafun na yanke hukunci. Gwawuna ya nuna kwarewa lokacin da yake shugaban karamar hukuma, kwamishina da kuma mataimakin gwamna, ya yi kokari sosai a mukaman da ya ruke.” Inji shi. 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here