Gwamna Zulum ya sake tsugunar da iyalai 6,000 da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu

WhatsApp Image 2025 05 05 at 11.44.02 750x430

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sanar da sake tsugunar da iyalai 6,000 da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.

Iyalan galibi sun fito ne daga kananan hukumomin Dikwa da Mafa.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa Zulum ya sanar da shirin ne a ranar Litinin a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna, daya daga cikin mafi girma da iyalai kusan 11,000 ke fakewa saboda rikicin da aka kwashe shekaru 10 ana yi a Borno.

Da yake jawabi ga manema labarai, Zulum ya sake nanata cewa sake tsugunar da su ya zama wajibi saboda yawaitar ayyukan baɗala a sansanin.

Karin karatu: Tawagar ƙwararru ta NAHCON ta tashi zuwa Makkah domin kaddamar da aikin Hajji

“Ba za a taba kawar da Boko Haram ba, ba tare da an sake tsugunar da jama’a ba, dole ne mutane su koma gidajensu su samu abin dogaro da kai, mun lura da cewa a sansanin ‘yan gudun hijira, ana samun karuwar karuwanci, kungiyoyin asiri, cin zarafin yara da sauran laifuka,” in ji Zulum.

WhatsApp Image 2025 05 05 at 11.44.03 768x503

Ya kara da cewa, “Idan za ku iya tunawa, kimanin shekaru hudu da suka wuce, mun sanar da cewa za a rufe dukkanin sansanonin ‘yan gudun hijira da ke cikin birnin Maiduguri, ya zuwa yanzu, mun rufe dukkaninsu, kusan 12 daga cikinsu, muna da sauran sansanoni guda biyu da suka rage.

A cewar Gwamna Zulum, kowanne daga cikin iyalai 6,000 za su samu tallafin abinci, da kayayyakin matsuguni, da kuma samun ayyukan kula da lafiya a wani bangare na shirin sake tsugunar da su.

WhatsApp Image 2025 05 05 at 11.44.00 768x538

Gwamnan ya kuma bayyana cewa yayin da kowane mai gida zai karbi Naira 100,000, za a raba wa matan gidan karin Naira 50,000.

A halin da ake ciki, Gwamna Zulum ya kuma bayyana wani shiri na inganta cibiyar koyar da sana’o’i da ke Maiduguri domin rage masu aikata laifuka da kuma rage fursunoni sanadiyyar aikata miyagun laifuka.

Karanta: Ɗalibai 420,415 cikin su miliyan 1.95 ne kaɗai da suka rubuta UTME suka samu maki sama da 200 – JAMB

Gwamnan, wanda ya ziyarci wurin a safiyar ranar Litinin, ya jaddada cewa ainihin hukuncin gidan yari shine canza rayuwa, ba wai kawai a tsare mutane ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here