Sarkin Kano Sanusi ya bayyana dalilan da suka sa Jonathan ya dakatar da cire tallafin man fetur

Muhammadu Sanusi II 720x430

Sarkin Kano na 16 a Daular Fulani, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya dakatar da shirin cire tallafin man fetur a shekarar 2012 ne saboda tsoron hare-haren kunar bakin wake na Boko Haram kan masu zanga-zanga, ba wai saboda adawa daga jama’a ba.

Sanusi wanda a wancan lokaci shi ne gwamnan babban bankin Najeriya, ya ce shi ne ɗaya daga cikin manyan masu fafutukar a soke tallafin, amma an yi kuskuren fahimta da kuma aiwatar da manufar.

Ya yi wannan bayani ne a ranar Talata yayin taron “Oxford Global Think Tank Leadership Conference” mai taken “Jagora Nagari Don Samar da Nagartacciyar ƙasa,” kamar yadda gidan talabijin na Arise TV ya ruwaito.

Sanusi ya bayyana cewa abin da ake kira tallafin man fetur a Najeriya, a gaskiya tsari ne ba tare da wata hanya ta rage haɗari ba,“naked hedge” ne, inda gwamnatin tarayya ke tabbatar da farashin man fetur a matakin da aka kafa ko da kuwa farashin danyen mai, canjin kudi ko ribar bashi sun tashi a kasuwannin duniya.

Wannan, a cewarsa, ya sa gwamnati ke kashe kuɗi masu yawa wajen kula da farashin, har ta kai ga aro kuɗi don biyan tallafin da kuma biyan ribar waɗannan bashin.

Ya ƙara da cewa da gwamnatin Jonathan ta aiwatar da cire tallafin a 2011, halin tattalin arzikin ƙasar yanzu zai fi sauƙi.

Ya bayyana cewa a lokacin, babban banki ya yi hasashen cewa hauhawar farashi zai tashi kaɗan kawai, sannan za a iya daidaita shi daga baya, sabanin matsanancin hauhawa da ake fuskanta yanzu.

Sanusi ya ce tsaron jama’a ne ya sa Jonathan ya dakatar da cikakken cire tallafin, domin gwamnati ta ji tsoron cewa idan kunar bakin wake ɗaya ya kai hari a wurin masu zanga-zanga a Kano, Legas ko Kaduna, abin zai rikide zuwa bala’i mai girma.

Duk da haka, Sanusi ya yaba wa Jonathan bisa jajircewarsa wajen ƙoƙarin aiwatar da gyaran tattalin arziki duk da haɗarin da ke tattare da shi.

Sarkin ya soki halayen wasu daga cikin shugabannin ƙasa da ya ce suna watsi da ƙimominsu da gaskiya saboda son kai da neman kuɗi, inda ya jaddada cewa yawancin masu ilimi suna rayuwa tamkar marasa ilimi saboda rashin daidaito da riƙon amana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here