‘Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarki da Fadawa a Taraba

b802c0d0 9eed 11ee b9a7 c91b9dfa91e5
b802c0d0 9eed 11ee b9a7 c91b9dfa91e5

Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 23 ciki har da basarake mai daraja ta biyu da fadawansa a karamar hukumar Yorro ta jihar Taraba.

Lamarin ya afku ne a daren ranar Talata inda ‘yan bindigar masu yawan gaske suka shiga garin tare da kewaye shi.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa, ba su san adadin ‘yan bindigar da suka shiga garin ba saboda yawansu.

Ya ce,” sun shiga cikin dare suka dauki na dauka suka bar na bari, kuma a cikin wadanda suka dauka baya ga basaraken da dogarinsa, akwai limamin masallacin Jumma’a da fastoci biyu da kuma sauran jama’ar gari.”

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun fasa shaguna tare da satar kayan abinci da abubuwan sha.

“Ba wannan ne zuwan su na farko ba, wannan shi ne karo na hudu da suka je garinmu” In ji mazaunin garin na Pupule.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta Taraba ta ce ta fara bincike tare da neman mutanen da aka sace.

Karanta wannan: Majalisar Dokokin Adamawa ta amince da kasafin shekarar 2024

Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Usman Jada, ya ce suna samun labarin abin da ya faru nan da nan kwamishinan ‘yan sandan jihar ya tura wani sashe na musamman da ke kula da masu satar mutane domin su je garin da kuma bin sawun ‘yan bindigar.

Ya ce an baza jami’an tsaro a jejin domin neman mutanen da aka sace, “amma har yanzu ba mu ji komai ba,” a cewarsa.

Jama’ar garin na Pupule dai, sun ce a duk hare-haren da aka kai masu sau uku a can baya, wannan shi ne mafi muni da tayar da hankali.

Kazalika al’ummar yankin sun yi kira da a girke musu karin jami’an tsaro a yankin.

Matsalar tsaro dai na ci gaba da zama ruwan dare a yankunan arewa maso yammacin kasar nan da kuma wasu yankuna na arewa maso gabashin kasar.

Kuma duk da kokarin da gwamnatin tarayyar kasar ta ce tana yi don kawo karshen wannan matsala har yanzu ba ta sauya zani ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here