Majalisar Dokokin Adamawa ta amince da kasafin shekarar 2024

Governor Fintiri 1536x1024
Governor Fintiri 1536x1024

Majalisar dokokin jihar Adamawa ta amince da kasafin shekarar 2024 da ya kai naira biliyan 225 da 893, kamar yadda gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya gabatar.

An amince da kasafin ne bayan gabatar da yadda za’a kashe kudin tare da yin la’akari da rahoton kwamitin kasafin kudi na majalisar.

Karanta wannan: Gwamnatin Kano za ta yi bincike akan gobarar Sakatariyar Gwale

Da take jawabi yayin nazarin rahoton, shugabar masu rinjaye, Kate Raymond Mamuno, ta yaba wa kwamitin bisa kwazon da ya yi.

Ta kuma yi kira ga majalisar da ta tabbatar da cewa dukkan ma’aikatu da hukumomi sun bi shawarwarin da aka zayyana a cikin rahoton yayin aiwatar da kasafin kudin.

Sauran ‘yan Majalisar da suka yi tsokaci kan rahoton sun hada da Yohanna Sahabo Jauro, daga mazabar Mubi ta Kudu.

Dokokin

Yayin karanta rahoton kwamitin samar da kayayyaki, shugaban majalisar Rt. Hon. Bathiya Wesley, ya bayyana cewa kudaden da ake kashewa yau da kullum sun kai Naira Biliyan 111 da miliyan 379.

Ya umarci akawun Majalisar da ya samar da kwafin kudirin amincewar ga Gwamna Fintiri bayan karatu na uku.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here