Gwamnatin jihar Kano tace za’a gudanar da tsatstsauran bincike akan musabbabin tashin gobara a sakatariyar karamar hukumar Gwale.
Mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyara gurin da lamarin ya faru.
Yace ya ziyarci wajen ne domin duba irin asarar da aka tafka a lokacin da aka samu iftila’in tashin gobarar.
Karanta wannan: Jami’ar Bayero ta horas da Matasa domin zama Shugabanni Nagari
Ya kuma tabbatarwa da al’umma cewa gwamnati za ta hada kai da rundunar ‘yan sanda, domin kama duk wadanda suke da hannu a tashin gobarar.
Acewarsa kuma da zarar an kammala bioncike za su girbi abinda suka shuka.