Shugaban kasa Bola Tinubu a daren ranar Litinin ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kasar ba za ta taba bari masu kokarin haddasa rashin zaman lafiya su rusa zaman lafiya, hadin kai da ikon kasar ba, yana mai cewa za a doke ‘yan ta’adda.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin shugabannin addinai da na gargajiya a wajen buda baki na hadin gwiwar addinai da aka gudanar a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
Ya amince da muhimmiyar rawar da shugabannin addinai da na gargajiya ke takawa wajen inganta zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma jagoranci na kyawawan dabi’u a cikin al’ummominsu.
Ya bayyana cewa kasar na fuskantar kalubale amma ‘yan ta’addan sun kara tsananta hare-hare saboda suna fuskantar matsin lamba da shan kaye a hannun jami’an tsaro.
Ya jaddada cewa Najeriya ba za ta taba mika wuya ba, kuma gwamnati ba ta karaya ba kuma za ta yi nasara a yaki da ‘yan ta’adda.
Shugaban kasar ya kuma yi alkawarin ci gaba da amfani da damar da aka ba shi domin karfafa tattalin arziki da inganta walwalar jama’a.
Ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar ya fara samun sauki, inda ya ce ana ganin sauyi mai kyau kuma masu karbar fansho suna fara samun sassauci.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta dauki muhimman matakai domin daidaita kudaden gwamnati tare da kauce wa rugujewar tattalin arziki.
Tinubu ya ce gwamnatin sa ta ceci Najeriya daga durkushewar tattalin arziki duk da cewa lokacin da suka karbi mulki kalubalen ya yi tsanani.
Ya kara da cewa a yanzu babu wani gwamnan jiha da ke wahalar samun rance daga bankuna domin biyan albashin ma’aikata.
Shugaban kasar ya sake jaddada kudirinsa na kara zuba jari a muhimman fannoni kamar noma da ilimi.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da kada su yanke kauna, yana mai cewa gwamnatin sa na ci gaba da kokarin gina kasa mai tsaro, zaman lafiya da wadata.
A nasa bangaren, Sarkin Nupe Alhaji Yahaya Abubakar ya gode wa shugaban kasar bisa gayyatar shugabannin manyan addinai biyu wajen buda baki.
Ya bayyana cewa taron alama ce ta hadin kai tare da yi wa kasar da shugabanninta addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da shiriya daga Allah.
Shi ma shugaban kungiyar Kiristoci CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya tabbatar wa shugaban kasa goyon bayan coci wajen kokarin karfafa tattalin arziki da tsaro.
Okoh ya wakilci shugaban cocin ECWA, Dr Stephen Baba-Panya.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa sarakunan gargajiya da shugabannin addinai daga yankuna shida na kasar sun halarci taron.












































