Babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin ta sanya ranar 18 ga watan Mayu domin fara shari’ar wani mutum mai suna Innocent Chukwuma wanda ya yi amfani da shafinsa na sada zumunta domin kira ga sojoji su hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta dage sauraron karar bayan wata bukata daga lauyan masu gabatar da kara, David Kaswe, wanda ya nemi karin lokaci domin nazarin takardun shari’ar.
Kaswe ya bayyana wa kotun a lokacin da aka ci gaba da sauraron karar cewa yanzu ne kawai aka sanar da shi game da lamarin bayan an tura takardun shari’ar zuwa ofishinsa daga Hukumar tsaro ta farin kaya.
Ya nemi a dage shari’ar domin samun damar nazarin takardun, inda mai shari’a Abdulmalik ta dage shari’ar zuwa ranakun 18 da 19 ga watan Mayu domin fara shari’a.
An gurfanar da Chukwuma a gaban kotun ne kwanan nan bayan wani sako da ake zargin ya wallafa wanda ke tunzura mutane.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa jami’an Hukumar tsaro ta farin kaya sun bi sahunsa har zuwa Oyigbo da ke Port Harcourt a jihar Ribas inda aka kama shi.
Lambar shari’ar da ke gaban mai shari’a Abdulmalik ita ce FHC/ABJ/CR/610/2025 tsakanin Tarayyar Najeriya da Innocent Chukwuemeka Onukwume.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na “X” mai suna @TheAgroman, Chukwuma ya bayyana cewa ana bukatar juyin mulki a Najeriya tare da kira ga sojoji su dakatar da gwamnatin Najeriya.
Ya kuma kara wallafa cewa ana bukatar juyin mulki a Najeriya, a kawar da APC, a dakatar da gwamnatin Najeriya sannan a shiga kungiyar AES, yana mai cewa wannan ne kawai abin da ake bukata a yanzu.













































