Kaduna: El-Rufai ya hana yin zanga-zangar addini

Nasir El Rufai 1
Nasir El Rufai 1

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya bai wa jami’an tsaro umarnin daƙile yin zanga-zangar da ke da alaƙa da addini musamman kan kalama ɓatancin da wata ɗaliba ta yi ga Manzon tsira a Sokoto.

Wannan dai na ƙunshe a cikin wata sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gida da harkokin tsaron jihar ta fitar da yammacin yau Asabar mai ɗauke da sa hannun kwamashinan ma’aikatar Samuel Aruwan.

A cewar sanarwar gwamnatin ta ɗauki matakin ne bisa yuƙurin wasu mutane na yunƙurin shirya zanga-zanga kan lamarin.

Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna El-Rufai, ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar sun daƙile duk wata zanga-zangar addini a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here