Gwamnatin jihar Sokoto, ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a ɗaukacin jihar sakamakon sauyawar zanga-zanga zuwa tarzoma.
Gwamnatin ta bayyana saka dokar ne a sanarwar da ta wallafa a shafinta na Facebook.
Haka kuma a cewar sanarwar dokar za ta fara aiki nan take daga lokacin wallafa ta.
A cewar gwamnatin jihar ta Sokoto ta ɗauki matakin ne domin dawo da zaman lafiya a jihar tare da tabbatar ingantuwar tsaro, bisa zanga-zangar da matasa suka yi a yau Asabar wadda ta koma tarzoma.













































