Bayan da Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa ASUU nan bada jimawa ba zata kawo karshen yajin aikin da ta shafe tsawon watanni 3 tana yi, a ranar Juma’ar nan.
Yanzu haka Kungiyar ta ASUU ta musanta labarin cewa za ta janye yajin aikin da take yi nan ba da jimawa ba.
Shugaban kungiyar mai kula da shiyyar Kano Farfesa Abdulkadir Muhammad, shi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Manema labarai.
“Ba mu da wani shiri na janye yajin aiki yanzu, hasalima babu wani taron tattaunawa da muke yi a halin yanzu”.
“Muna da tsari na sanar da abubuwan da muke aiwatarwa, ya kamata mutane su gane akwai matakai da muke bi wajen sanar da yajin aiki, don haka wannan labari ba Gaskiya ba ne”. Inji Abdulkadir.
“Mambobinmu sun bukaci cewa kada ma ayi tunanin za a kira su a nemi shawarar su har sai gwamnati ta biya musu bukatunsu, wanda kuma har yanzu gwamnatin ba ta da wani yunkuri na yin hakan”.
A ranar Juma’ar nan ne dai wata jaridar Internet mai suna DAILY POST ta wallafa labarin cewa, kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU za ta janye yajin aikin da ta shafe watanni 3 tana yi nan ba da dadewa ba.













































