Hukumar kula da jami’o’i ta kasa ta bayar da umarnin rufe jami’o’in kasar nan domin baiwa dalibai damar shiga zaben shekarar da muke ciki ta 2023.
A wata wasika da hukumar ta NUC ta aikewa shugabannin jami’o’i da daraktocin cibiyoyi na jami’o’i, NUC ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan umarnin ministan ilimi Adamu Adamu.
A ranar 25 ga watan nan da muke ciki na Fabrairu ne za’a fara gudanar da babban zaɓen kasar nan.













































