Rundunar ƴan sanda a jihar Enugu ta ce ta kama wata mata da ta fito a wani faifan bidiyo da ake zargin ta da karbar kudade kafin ta ba masu su katin zabe katin su.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansanda a jihar, DSP Daniel Ndukwe, ya fitar yau Alhamis a Enugu.
“Jami’an ƴan sanda da ke aiki a sashin binciken manyan laifuka na jihar Enugu, a ranar 31 ga watan Janairu, 2023, sun kama wata mata da ake zargi, Chinwendu Nnamani, mai shekaru 41.
“Nnamani na da hannu a cikin wani faifan bidiyo na kafafen sada zumunta wanda aka gan ta ana zarginta da sayar da katunan zabe na dindindin (PVCs) na INEC akan kudi Naira Dubu daya a wata makarantar firamare da ke Emene, Enugu.
“Haka kuma an kama wata Nkiruka Patience Obinna, mai shekaru 38, wadda aka bayyana a matsayin ma’aikaciyar INEC, kuma ana zarginta da bayar da irin wadannan PVCs ga wanda ake zargi na farko don rabawa ga ainihin masu su.
“An kammala bincike, an gurfanar da karar a gaban kotu bisa tanadin dokar zabe ta 2022, kuma wadanda ake zargin sun gurfana a gaban kuliya,” in ji shi.
Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa, an bayar da belin waɗanda ake zargin, kuma an dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu domin ci gaba da shari’ar.












































