Gwamnatin Jihar Kano ta rushe wasu gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a wani fili da ke yankin Sharada a ƙaramar hukumar Gwale, tare da gargadin cewa za a gurfanar da mutanen da ke da hannu a aikin.
Kwamishinan ma’aikatar ƙasa da tsare-tsaren gine-gine, Abduljabbar M. Umar, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani aikin sa ido kan gine-gine a wani yanki daga gefen ofishin ‘yan sanda na Sharada zuwa Kwanar Ganduje.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta gano cewa wasu mutane sun fara gina gine-gine a kan filin ba tare da izini ba.
Ya bayyana cewa tun asali an ware filin ne domin zama wurin shakatawa ga mazauna gidajen Hukumar gidaje ta tarayya da ke yankin.
Ya kuma ce wannan fili ya kamata ya kasance wurin shakatawa da lambun nishadi mallakin mazauna yankin da ƙungiyarsu, inda iyalai za su rika zuwa domin hutawa.
Sai dai ya nuna damuwa cewa wasu marasa gaskiya tare da goyon bayan wasu mutane sun yanke shawarar mayar da wurin zuwa kasuwanci.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta gano wasu sun fara gina shaguna da wasu gine-gine a wurin, lamarin da ya bayyana a matsayin haramtacce.
Ya jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da sauya wannan fili zuwa mallakar kasuwanci ta kashin kai ba, yana mai cewa duk wani gini a Kano dole ne ya bi ƙa’idojin da aka shimfiɗa.
Ya ce duk wanda ke son yin gini dole ne ya samu amincewa daga Hukumar tsarawa da raya birane ta Kano, yana mai cewa duk wani gini da aka yi ba tare da izini ba ana ɗaukar sa a matsayin haramtacce.
Ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa za a ci gaba da sanya ido a wurin domin hana sake faruwar irin wannan gini ba bisa ka’ida ba.
Ya ƙara da cewa gwamnati na da shirin mayar da filin zuwa wurin shakatawa domin amfanin al’umma.
Ya ce ana kan tantance takardun da suka shafi mallakar filin, tare da jaddada cewa duk mai hakkin mallaka dole ne ya tabbatar an yi amfani da filin a matsayin wurin shakatawa.













































