Tinubu ya rage tawagar Jami’an da za su rinka raka shi kasashen waje

Tinubu, kasar, Qatar, Najeriya, Legas, kasuwanci
A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu zai bar Najeriya zuwa kasar Qatar bisa gayyatar Sheikh Tamin Al-Thani sarkin Qatar.Kamar yadda Ajuri Ngelale, mai...

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da rage kashi 60 cikin 100, na jami’an da suke rufa masa baya a tafiye-tafiyen aiki na gida da kasashen waje.

Mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaba kasa da ke Abuja.

Karanta wannan: Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin bana

yace umarnin ya shafi ofisoshin shugaban kasa da mataimakinsa sai matar shugaban kasa da matar mataimakinsa, da dukkan ma’aikatu da sassan da hukumomi.

Ngelale ya ce ofishin matar shugaban kasa da na matar mataimakin shugaban kasa ya takaita ga ‘yan rakiya 10 a tafiye-tafiyen aiki a cikin kasar.

Karanta wannan: Gwamnati ta dakatar da biyan mafi karancin Albashi-TUC

Yayin da ofishin mataimakin shugaban kasar zai takaita ne ga ‘yan rakiya 15 a tafiye-tafiyen aiki a cikin kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce a yanzu ministoci sun takaita ne kawai ga ‘yan rakiya mutum hudu, yayin da shugabannin hukumomi kuma suka takaita ga iya mutum biyu.

Karanta wannan: Yanzu-yanzu: Betta Edu ta isa Hukumar EFCC don amsa tambayoyi

Wannan lamari ya zo ne makonni hudu bayan gwamnatin Tinubu ta fuskanci kakkausar suka kan halattar taron COP28 da ya gudana a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, da ayarin ‘yan rakiya masu yawan gaske.

Muna tafe da Karin bayani…..…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here