‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dan sanda a jihar Kwara

police officers 750x430 1
police officers 750x430 1

‘Yan bindiga sunyi garkuwa da wani dan sanda mai suna ASP Abdulmumini Yusuf, wanda yake aiki a Ilorin dake jihar Kwara.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Paul Odama, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN faruwar lamarin ranar Aalhamis a Ilorin.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Okasanmi Ajayi, ya ce sunan sun gudanar da binkice domin kubutar dashi.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaitu cewa lamarin ya faru ranar Talata da daddare, yayin da jami’in yake kokarin shiga gidan sa da yake unguwar Ogidi dake Ilorin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here