Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da nadin Oba Moshood Aliiwo, Olubadan na Ibadan a matsayin uban jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi mallakin jihar da ke Kumbotso.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan bayan taron majalisar da aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnati.
Muhammad Garba ya ce, majalisar ta kuma amince da nadin Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban INEC a matsayin shugaban majalisar gudanarwar jami’ar.
Haka kuma Ya ce, hakan ya biyo bayan samun lasisin gudanar da jami’ar daga hukumar kula da Jami’o’i ta Kasa NUC, wadda ta amince da ita a matsayin jami’ar Jiha ta 61 da jami’a ta 222 a tsarin jami’o’in Najeriya.
Sauran ‘yan majalisar sun hada da Dr Muhammad Kwankwaso da Hajiya Zulaiha Ahmed da Dr Ibrahim Wunti sa iDr Halima Muhammad da Alhaji Sabi’u Bako.
Kwamishinan ya kuma ce, nadin ya zo dai-dai da kashi na uku na sashe na 22 na Jami’ar Ilimin ta Sa’adatu Rimi.
Ya kuma bayyana cewa “Za a samu majalisar da za ta zama hukumar gudanarwar jami’ar”, yayin da sashe na daya da na biyu da kuma na uku na jadawalin doka ta biyu ya tanadi cewa “Dr. Abdullahi Ganduje zai nada shugabannin gudanarwar jami’iar.
Muhammad Garba ya kara da cewa, bisa ga sashe na 3, (2) a jadawali na biyu, iyayen jami’ar za su ci gaba da rike mukaman su har na tsawon shekaru hudu, wanda za a sabunta musu zuwa karo na biyu kuma na karshe na wasu shekaru hudun.
Haka kuma, Ya ce sauran wadanda aka nada sun hada da Farfesa Isa Bunkure, a matsayin sabon shugaban jami’ar sai Dr. Kabiru Gwarzo, a matsayin Mataimakin shugaban Jami’ar da Dr Miswaru Bello, a matsayin mataimakin shugaban jami’ar a fannin gudanarwa da Saminu Bello Zubairu, a matsayin magatakarda da Ibrahim Yahaya a matsayin akawun jami’ar sai kuma Mabruka Abubakar Abba a matsayin shugaban sashen dakin karatu.
NAN










































