Gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana fita a yankunan Chikun

06c9e227 nasir el rufai
06c9e227 nasir el rufai

Gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana fita a yankunan Chikun

Gwamnatin jihar Kaduna, ta sanar da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 nan take a yankin Sabon Garin Nassarawa da Tirkaniya a ƙaramar hukumar Chikun.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar a yau Litinin.

Sanarwar ta ce, “An cimma wannan matsaya ne biyo bayan taɓarbɓarewar doka da oda da ta kai ga kashe wasu mutane biyu a wani rikici da ya ɓarke a garuruwan”.

Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa, “An umurci hukumomin tsaro da su aiwatar da dokar hana fita a yankunan, domin dawo da zaman lafiya yayin da ake ci gaba da bincike”.

“Don haka an yi kira ga al’ummar yankunan da su yi biyayya ga dokar hana fita a yankunan wadda ta fara aiki nan take”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here