Sojoji sun kashe yan bindiga 11 a Kaduna

army kaduna dsa
army kaduna dsa

Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce wasu dakarun sojin na musamman sun kashe ‘yan bindiga 11 a wani artabu da suka yi da su a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa yankin Birnin Gwari ya kasance wani babban sansani ga ‘yan fashi da makami, inda akasarin matsalar garkuwa da mutane ke faruwa a yankin.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya tabbatar da kashe ‘yan bindigar 11 a wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi a jihar.

Aruwan ya ce, binciken da gwamnatin jihar Kaduna ta gudanar ya nuna cewa sojojin sun zarce zuwa wasu wuraren da aka gano, tare da fatattakar ‘yan ta’adda a garuruwan Bagoma da Rema da Bugai da Dagara sai Sabon Layi da Gagumi da Kakangi da Katakaki da kuma Randagi.

Ya ƙara da cewa, a yayin gudanar da wadannan ayyuka, sojojin sun tuntubi ‘yan bindiga a Kakangi da Katakaki.

“An gwabza kazamin luguden wuta yayin da sojojin suka samu nasarar fatattakar bata garin.

“An tabbatar da kashe ‘yan bindiga 11, yayin da wasu suka gudu.

“Bayan nan kuma, Sojojin sun yi nasarar kwato bindigogi kidar AK-47 guda biyu da gidan harsasai da kuma harsashi masu rai guda 57,” in ji shi.

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana jin dadinsa da irin namijin kokarin da sojojin ke yi.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here