Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da kafa kwamitin binciken domin binciken abin da ya yi sanadiyyar mutuwar daliba a sakandiren St. Louis da ke Kano.
Hakan na cikin wata sanarwar da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis.
SolaceBase ta rawaito cewa Kwamishinan Ilimi, Alhaji Ali Haruna Makoda ne zai jagoranci kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Barr. Aminu Hussain, mai bai gwamna shawara ta musamman kan harkokin shari’a, Barr. Hamza Dantani, Baba Abubakar Umar sakatare hukumar kula da makarantu masu zaman kansu, Sunusi Bature Dawakin Tofa darakta janar n yada labarai, Liman Ahmed Zubairu, shugaban kungiyar iyayen daliban St. Louis Kano, Hafsat Aminu Adhama da Binta Abdullahi Mukhtar.
An baiwa kwamitin aikin gudanar da bincike mai zurfi na gaskiya kan abin da ya haifar da mutuwar dalibar, tare da gano abubuwan da suka faru a lokaci da duk wani rauni a bangaren kula, jin dadin dalibai ko hanyoyin gudanarwa na makaranta.
Gwamna Yusuf ya sake nanata aniyar gwamnatin sa na tabbatar da an gano gaskiya kan lamarin kuma a dauki matakan da suka dace domin hana sake faruwar haka.
Ya umarci mambobin kwamitin su gudanar da ayyukansu cikin adalci, kwazo da kwarewa don tabbatar da adalci da tsaron dukkan dalibai.
Ana sa ran kwamitin zai mika sakamakonsa da shawarwarinsa ga gwamnatin jihar cikin wa’adin da aka ba shi.













































