Yayin da kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU ta kara watanni 2 kan Yajin aikin da take yi, Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan wannan karin wa’adin da ta ce ta biya dukkan bukatun kungiyar.
Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya mayar da martani ga sanarwar daftarin kundin a wata hira da manema labarai a karshen taron tunawa da Commonwealth na shekarar 2022 a Abuja ranar Litinin.
Nwajiuba, wanda ya dage kan cewa gwamnatin tarayya ta biya dukkan bukatun kungiyar, ya kara da cewa an saki dukkan alawus-alawus da kuma kudaden farfado da su.
“ASUU ta sanar kuma mun hadu da duk abin da suka nema, mun yi dukkansu ciki har da alawus-alawus din da aka samu da asusun farfado da su; sun zabi a tsawaita shi na tsawon watanni biyu,” inji shi.
Idan za a iya tunawa, kungiyar jami’o’i bayan karewar yajin aikin farko na wata daya a ranar 14 ga Maris, ta ayyana yajin aikin na wasu watanni biyu.
Kungiyar ta ASUU ta kuma zargi gwamnatin tarayya da yunkurin kin amfani UTAS, tsarin biyan kudi da ASUU ta tsara a madadin tsarin biyan kudin IPPIS.













































