‘Yan Sanda sun kama matar da ake zargi da yanke al’aurar saurayinta a Kano

Police badge

Rundunar ‘yan Sandan Jihar Kano ta kama wata mata Maimunatu Idris mai shekaru 25, da ake zargi da kai wa saurayinta hari da wuka tare da yanke masa al’aura a dakin otal a Kano.

Ana zargin mai laifin, wadda ‘yar asalin Karamar Hukumar Maigatari ce ta Jihar Jigawa, da aka kama bayan afkuwar lamarin a otal din Durbar da ke yankin Badawa na Kano.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa matar ta kai harin ne bayan ta gano cewa saurayinta yana niyyar auren wata mace daban.

A cewar ‘yan sanda, Babban Baturen ‘Yan Sanda na Badawa ne ya jagoranci tawagar masu bincike zuwa otal din bayan samun rahoton faruwar lamarin. An kama wanda ake zargin a wurin, sannan aka kwato wukar da ake zargin ta yi amfani da ita a matsayin hujja.

An gaggauta kai wanda aka cutar zuwa Asibitin Abubakar Imam da ke Kano, inda yake samun magani. Yayin da suka ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya yi tir da harin, ya kuma gargadi jama’a da kada su dauki doka a hannunsu.

Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar za ta gudanar da cikakken bincike kuma za ta tabbatar an gurfanar da duk wanda aka samu da laifi bisa doka.

An samu labarin cewa mai laifin ta gayyaci saurayinta su je otal bayan ta gano yana shirin kawo karshen alakar su da zummar auren wata macen daban.

A cewar wata shaidar gani da ido, matar ta yi amfani da wannan dama ta kai wa wanda aka cutar hari kafin a shawo kanta aka mika ta ga ‘yan Sanda, yayin da aka kai wanda ya jikkata asibiti don jinya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here