Jaridar Tribune ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren Asabar ɗin da ta gabata ne ɓata garin suka kutsa cikin garin suka yi ta harbe-harbe inda suka samu mutane tara wanda shida daga ciki suka mutu nan take yayin da 3 kuma suke cikin mawuyaci hali.
Jaridar Tribune ta kuma ruwaito cewa, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar mata da faruwar lamarin yana mai cewa, tuni suka duƙufa wajen ceto Dagacin.












































