Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana baƙin cikinta kan mutuwar ‘yan sanda uku da suka rasu suna bakin aiki kwanan nan.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa ’yan sandan 3 daga Sashin Magance Bama-bamai (EOD) na Rundunar ’Yan Sanda ta Zamfara da suka yi shahada suna bakin aiki a ranar Litinin.
Jajirtattun jami’an sun rasu ne sakamakon fashewar wata na’urar fashewa da aka kera (IED) da ‘yan bindiga suka dasa a kan hanyar Anka-Bagega da ke Karamar Hukumar Anka ta jihar.
A cewar majiyoyin tsaro da Zagazola Makama ya rawaito, wata jaridar yaki da ta’addanci, ta nakalto, lamarin ya faru da misalin karfe 5:05 na yamma a ranar 15 ga Yuni.
Jami’an sun kasance cikin tawagar da Abdulrazak Musa Hassan, jami’in da ke kula da sashin magance bama-bamai (EOD), ke jagoranta, wanda suka je don kawar da wata na’urar fashewa da ake zargi ’yan bindiga sun dasa.
“Tawagar, wadda ta hada da jami’an Sashin Mayar da Martani kan Manyan Laifuka (VCRU), an rawaito suna gudanar da aikin tsaftacewa da ke bada kulawa ta musamman suna cikin abin hawa mai sulke lokacin da abin hawan ya taba na’urar fashewar ba tare da sani ba,” in ji Makama.
“Fashewar ta haifar da mutuwar SP Abdulrazak Musa Hassan nan take, Inspector Murtala Musa na VCRU da Inspector Auwal Ahmad da ke sashin EOD.
“An kwashi gawarwakinsu zuwa Asibitin Kwararru na Tarayya (FMC) da ke Gusau, domin duba gawa.”
Sakatariyar Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Nakwada ne ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa wajen da aka gudanar da sallar jana’izar mamatan.
IGP Olatunji Disu ne ya jagoranci sallar a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sandan Gusau, bisa ga koyarwar addinin Musulunci.
Sakataren ya isar da sakon ta’aziyyar gwamnati da al’ummar jihar ga IGP, Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara, iyalai da jami’an ‘yan sanda baki daya.
Ya yi addu’ar Allah ya jikan mamatan da rahama ya ba iyalansu hakuri kan wannan babbar asara.
Ya kuma sake tabbatar da kudurin gwamnatin jihar na ci gaba da tallafa wa iyalai ‘yan jaruman da suka rasa rayukansu.
Nakwada ya kara jaddada kudurin gwamnatin na ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro domin fatattakar ‘yan bindiga da sauran laifuka daga jihar.
“Wannan bakin lamari ba zai sa mu daina ba, a maimakon haka ya kara mana karfin gwiwa. Za mu kara kokari, kuma nasara tabbatacce ce, In-Sha-Allah,” in ji shi. NAN












































