Shekarun haihuwa na bogi: Rundunar ‘yan sanda za ta gurfanar da tsohon mataimakin sufeto janar da kwamishinoni biyu masu ritaya

IGP Kayode Egbetokun PMF 750x430

Sufeto janar na ‘yan sandan kasar nan, kayode egbetokun, ya shigar da ƙara kan wasu tsoffin manyan jami’an rundunar ‘yan sanda bisa zargin ƙirƙirar shekarun haihuwa na bogi domin su ci gaba da zama a kan aiki.

An shigar da ƙarar me a kotun babbar birnin tarayya Abuja karkashin mai shari’a yusuf halilu, wanda ya sanya ranar 25 ga watan satumba domin gurfanar da waɗanda ake zargi.

Ƙarar mai shafi 14 ta haɗa da idowu owohunwa, tsohon mataimakin sufeto janar; benneth igwe da ukachi opara, tsoffin kwamishinonin ‘yan sanda; obo ukam obo, tsohon mataimakin kwamishina; da kuma simon lough, tsohon mataimakin kwamishina.

Haka kuma an ce akwai wasu da ba a kama ba.

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa owohunwa ya canza shekarun haihuwarsa a abuja a watan disamba 2024, inda ya ce an haife shi a ranar 20 ga watan yuli, 1970, maimakon shekararsa ta asali 1967.

Karin labari: Lagos: ’Yan sanda sun kama tsohon ɗan fursuna bisa zargin satar kayan ado na Zinare a Allen Avenue

Haka nan, an ce benneth igwe ya canza shekarar haihuwarsa daga 1964 zuwa 1968 tare da rikicewar rajistar shiga aiki, yayin da lough ya ƙirƙiri shekarun haihuwarsa a shekarar 2022 daga 1967 zuwa 1969.

Hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewa wannan ya saɓa wa dokokin ma’aikatar gwamnati kuma akwai hukunci a karkashin sassa na 97, 161, 366 da 158 na kundin hukunta laifuka.

Sai dai waɗanda ake zargin sun musanta laifin, suna masu cewa tuhumar ba ta da tushe illa siyasa ce kawai.

Waɗanda ake tuhuma sun ce ƙarar ta samo asali ne daga ƙungiyar matasan gaskiya mai zaman kanta ƙarƙashin jagorancin kelvin adegbenga, wadda ta kai ƙorafi kan su, daga bisani, sufeto janar ya aika musu da takardar tambaya a watan janairu 2025 bisa zargin cin zarafi.

Amsar owohunwa a ranar 16 ga watan janairu ta bayyana cewa kuskure ne aka yi a takardun ofis na manyan jami’an rundunar inda aka rubuta shekarar haihuwarsa 1970 maimakon 1967. Shima ya dage cewa ranar naɗa shi aiki a hukumance ta kasance 15 ga watan agusta, 1996.

Igwe da lough suma sun dage cewa sun kasance masu gaskiya, inda suka ce masu ƙorafin sun rikita bayanan aikinsu da tsarin makarantar koyon aiki ta gwamnati (ascon), wadda ke ba da damar a ɗaukaka wasu jami’ai da hakan ke haifar da sabbin bayanan aikin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here