Zababbun Sanatoci uku da suka fafata neman shugabancin majalisar dattawa ta 10 da za a kaddamar a watan Yunin 2023, sun janye takararsu tare da nuna goyon bayansu ga daya daga cikin ‘yan takarar Sanata Godswill Akpabio daga Akwa ibom.
Rahotanni sun bayyana cewa, hakan ya biyo bayan wata ganawar sirri ta sa’o’i biyu da zababbun sanatoci daga jam’iyyar APC mai mulki suka gudanar a gidan gwamnan jihar Ebonyi da ke Asokoro.
Bayanai sun ce tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa Sanata Jubrin Barau, da gwamnan jihar Ebonyi mai barin gado Dave Umahi sun sanar da cewa sun amince da dan takarar da aka amince da shi domin samun zaman lafiya da hadin kan kasa.
Mutanen uku sun kuma bayyana cewa taron ya yanke shawarar gabatar da Barau a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawan ta kasa.
A cewar Ndume, “Dukkanmu mun mika wa dan’uwanmu kasancewa awannan matsayi na shugaban majalisar dattawa na kasa ta 10. Mun san yana da ikon jagorantar Babbar majalisar.
Umahi ya ce, “Akpabio ya zo ne bayan sulhu, amma jiya, na ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na gayyatar ta, inda yacemin na janye takara dana keyi.
“Ya ce, Don Allah kar ku tsaya takara kuma duk an amince da Sanata Akpabio matsayin shugaban majalisar dattawa da kuma Sanata Barau a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa.”
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Akpabio ya bayyana jin dadinsa da amincewar da takwarorinsa suka ba shi, ya kuma yi alkawarin ba za su yi kasa a gwiwa ba a kokarin sa na ciyar da majalisar kasa gaba.
Bayan kammala wannan taro, Akpabio da tawagarsa sun sake yin wani taro da sabbin Sanatocin APC a Frazier Suites da ke Abuja.