
Kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa ya cire Sanata Ali Ndume na (APC, Borno ta Kudu) a matsayin babban mai tsawatarwar majalisar.
A cewar wasikar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, shugaban majalisar da Alhaji Umar Ganduje da sakataren kasa, Sanata Suŕajueen Basiru suka rubutawa shugaban majalisar dattawa, an kuma bukaci Ndume da ya fice daga jam’iyya mai mulki ya koma jam’iyyar PDP ko kuma wata jam’iyyar adawa.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Babbar kotun tarayya ta soke tsige Phillip Shuaibu
Jam’iyyar ta kuma maye gurbinsa da Sanata Mohammed Tahir Monguno na (APC, Borno ta Arewa).
Akpabio ne ya gabatar da bukatar a kada kuri’a, kuma dukkan Sanatocin APC sun tabbatar da hakan.