
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Laraba ta soke tsige Philip Shaibu a matsayin mataimakin gwamnan Edo.
Mai shari’a James Omotosho, a wani hukunci da ya yanke, ya bayar da umarnin mayar da shi ofishin ne bisa dalilin cewa majalisar dokokin jihar Edo ta ki bin ka’idar tsige shi.
Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa zargin da majalisar ta kafa a kan batun tsige shi bai cancanta a doka ba.
Karin labari: Hukumar zabe a Kaduna ta sanya ranar zaben Kananan Hukumomi
Don haka Alkalin ya umarci Sufeto-Janar na ’yan sanda da ya ba shi tsaro da ake bukata domin ya ci gaba da gudanar da ayyukan ofishin har zuwa karshen wa’adinsa.
Haka zalika, Justice Omotosho, ya ajiye nadin wani mataimakin gwamna a madadin Shaibu.
NAN ta rawaito cewa Shaibu, wanda ke gaban kotu, ya zubar da hawayen farin ciki da jin furucin alkalin.












































