Mataimakin gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi murabus daga muƙaminsa na kwamishinan noma da albarkatun ƙasa a yau Lahadi.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa kwamishinoni da dama da sauran masu rike da muƙaman siyasa na yin murabus bisa ga wa’adin da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayar na ajiye aiki ga masu rike da muƙamai zuwa ranar 18 ga watan Afrilu ko kuma kafin ranar kamar yadda dokar zaɓe ta sashe na 84 (12) da aka yiwa gyara a bana.
Wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Hassan Musa Fagge ya fitar ce ta tabbatar da murabus ɗin nasa.
“Godiya ta tabbata ga Allah maɗukakin Sarki da ya ba ni iko, hikima tare da yi mun jagora wajen tafiyar da ma’aikatar noma da albarkatun ƙasa tsawon shekaru bakwai a karkashin mulkin gwamnanmu Dakta Abdullahi Umar Ganduje,” in ji sanarwar.
“A cikin waɗannan shekarun, na yi aiki a matsayin Kwamishinan Noma a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje, na samu ilimi da dama, na faɗaɗa hangen nesa, na kuma samu gogewa wajen yi wa al’umma hidima.
“A cikin waɗannan shekarun mun yi aiki tare da hangen nesa kuma mun sami nasarori da dama a fannin aikin gona,”
“Na yaba da damar da aka bani na zama kwamishina a ƙarƙashin gwamnatin Ganduje wadda a yau ta sa na kasance cikin kwamishinonin noma da suka fi daɗewa a Najeriya.”
“Shawarar da na yi na yin murabus a matsayin kwamishinan noma da albarkatun ƙasa shi ne in ci gaba da harkokina na siyasa, Zan ci gaba da bayar da gudunmawar ci gaban jihar Kano.













































