Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin sake dawo da Tarihi a cikin manhajar ilimi na asali.
Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya tabbatar da umarnin da shugaban kasa ya bayar na maido da koyar da darasin Tarihi a makarantun firamare da sakandare a fadin kasar nan.
Da yake magana a yayin wani shiri na musamman na Bita na Karshen Shekara na Gidan Talabijin na Channels a ranar Talata, Alausa ya bayyana cewa, “Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a dawo da tarihin Najeriya a matsayin wani fanni na ilimi na asali.”