A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar karbar Korafe-korafen Jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta kama tare da tsare daraktan kula da ma’aikata, Ma’ajin, Kudi na karamar hukumar Nasarawa da babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar, Mustapha Maifada bisa zargin karkatar da Naira miliyan 105.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa SolaceBase cewa ma’aikatan hukumar uku an umurce su da su baiwa babban mataimaki na musamman Naira 105,000 don gabatar da wani shiri.
Duk da haka, an zarge su da bayar da chekin Naira miliyan 105 ga hadimin gwamnan tun watan Nuwamban 2024.
Karin labari: Gwamnatin Kano Ta Fito Da Sabon Shirin Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A jihar
Dangane da bayanan da aka samu daga wata tara da aka kafa kwamiti domin sa ido kan kudaden kananan hukumomi, hukumar ta fara gudanar da bincike kan zargin karkatar da kudaden.
Daya daga cikin majiyoyin ta shaida wa SolaceBase cewa a lokacin da ake bincike ma’aikatan hukumar da ake tsare da su sun yi ikirarin cewa an biya kudin ne bisa kuskure kuma lamarin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ki amincewa da shi duba da cewa an aikata laifin da ake zargin an aikata a watan Nuwamba da kuma wasu bayanai da ke hannunta.
Majiyar ta ci gaba da cewa, a binciken da ake yi, an gano cewa Mustapha Maifada ya sayi kadarori da kudin.
”Har yanzu ana ci gaba da bincike kuma ana iya gurfanar da su gaban kuliya bayan kammala bincike”.
Sai dai duk kiraye-kirayen da aka yi wa shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Muhuyi Magaji Rimingado bai yi nasara ba saboda layukan wayarsa ba sa tafiya.
Hakazalika ba mu samu mai magana da yawun hukumar Kabir Abba ba ta wayar hannu.