Jam’iyyar APC ta dage zaben fidda gwani na Majalisar Wakilai daga Juma’a, 15 ga Mayu, zuwa Asabar, 16 ga Mayu.
Wannan zaben na daga cikin shirye-shiryen babban zaben 2027.
Sakataren Yada Labarai na Ƙasa, Mista Felix Morka, ne ya sanar da sauya ranar a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.
“Ranaku da aka sanar a baya na zaben fidda gwani na Sanatoci, Majalisar Dokokin Jiha, Gwamnoni da Shugaban Kasa suna nan ba su canz ba,” in ji Morka.
Ya ce sabon jadawalin zai kasance kamar haka:
Majalisar Wakilai — Asabar, 16 ga Mayu.
Majalisar Dattawa — Litinin, 18 ga Mayu.
Majalisar Dokokin Jiha — Laraba, 20 ga Mayu.
Gwamnoni — Alhamis, 21 ga Mayu.
Shugaban Ƙasa — Asabar, 23 ga Mayu, 2026. (NAN)











































