An kama Sarakuna biyu da wasu mutum biyar kan harin tashar jirgin ƙasan Edo

326384000 528445235921726 8827600602887932658 n
326384000 528445235921726 8827600602887932658 n

Gwamnatin jihar Edo, ta ce ta kama sarakun guda biyu tare da wasu mutum biyar waɗanda ake zargi da hannu a garkuwa da fasinjoji 20 a hari kan tashar jirgin ƙasa a jihar ranar 7 ga watan Janairu.

Kwamishinan sadarwa da wayar da kai a jihar, Chris Nehikhare, shi ya bayyana hakan jiya a Benin yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan fitowa taron majalisar zartaswa.

Ya ce jami’an tsrao sun samu nasarar kuɓutar da mutum biyu da suka rage a hannun masu garkuwa da mutanen.

A ranar 7 ga watan Janairu ne, wasu da ake zargin ‘yan bindiga suka kai hari tashar jirgin ƙasa a jihar tare da sace mutum 20.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here