Dalilin da ya sa muka sauya wa Malam Abduljabbar Kabara gidan ajiya da gyaran hali – hukumar NCoS

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Hukumar kula da gidajen ajiyar da gyaran hali ta ƙasa reshen jihar Kano ta bayyana cewa sauya wa Malam Abduljabbar Nasiru Kabara matsuguni daga Kurmawa da ke Kano zuwa Kurkukun Kuje da ke Abuja, wata al’ada ce ta gudanarwa wadda ake yi bisa tsarin aiki na hukumar domin inganta tafiyar da harkokin fursunoni a ƙasar nan.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar a Kano, CSC Musbahu Lawan K/Nassarawa, ya fitar a ranar Laraba, hukumar ta ce an yi wannan canjin ne a ranar Talata bisa tanadin dokar hukumar gyaran hali ta ƙasa ta shekarar 2019, domin aiwatar da nauyin da doka ta ɗora mata na kula da fursunoni yadda ya kamata.

Hukumar ta bayyana cewa irin wannan sauyi al’ada ce da ake yi lokaci zuwa lokaci, bisa la’akari da abubuwa kamar tsaro, irin fursunan da ake tsare da shi, ƙarfin wuraren tsarewar, da kuma bukatar gyara da koyar da sana’o’i.

A watan Disamba na shekarar 2022, babbar kotun jihar Kano ta samu Malam Abduljabbar, malamin addinin Musulunci, da laifin ɓatanci ga Annabi kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Tun daga lokacin yake tsare yana jiran sakamakon ƙarar da ya shigar da neman daukaka hukunci.

Canjin wurin tsarewar Malam Abduljabbar zuwa Kuje ya jawo cece-kuce a tsakanin jama’ar Kano, inda mutane da dama ke tambayar dalilan da suka sa aka dauki wannan mataki.

Sanarwar ta kara da cewa, jukumar na tabbatar wa jama’a cewa an kiyaye dukan haƙƙoƙin Malam Abduljabbar bisa doka, kuma wannan canji bai shafi matsayin shari’arsa ba, haka kuma bai hana shi damar daukaka ƙara ko samun taimakon lauya ba.

Shugaban hukumar gyaran hali ta jihar Kano ya nanata kudirin hukumar na ci gaba da tabbatar da tsare masu laifi cikin aminci, gyara.musu hali da mayar da su cikin al’umma domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here